1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

061211 Syrien AL Beobachter

December 6, 2011

Duk da koƙarin mayar da Siriya saniyar ware da ƙasashen duniya ke yi, ana cigaba da fuskantar rikici a ƙasar tsakanin jami'an tsaro da masu boren adawa da bukatar sauyin gwamnatin Bashar al-Assad

https://p.dw.com/p/13NYF
Bashar AssadHoto: AP

Gwamnatin Siriyan dai ta sanar da amince wa masu gani da ido shiga cikin ƙasar, wanda ke ɓangaren ka'idojin da kungiyar ƙasashen larabawa suka gindaya, adaidai lokacin da kungiyoyin kare hakkin jama'a suka ruwaito cewar dakarun gwamnati sun kashe fararen hula 'yan adawa 34, tare da jibge gawarwakinsu kan titi.

To sai dai a wasikar da ta aikewa kungiyar kasashen larabawan, gwamnati na Siriya tace a shirye take tayi maraba masu bincike zuwa cikin kasar, idan an cikanta mata nata ka'idoji, kamar yadda kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Jihad Makdisi ya shaidar.

Arabische Liga Ägypten Nabil al-Arabi
Nabil al-ArabiHoto: picture alliance/dpa

" Siriya na muradin rattaba hannu akan jaddawalin kungiyar kasashen larabawa. Muna bayyana kyakkyawar manufarmu.SAi dai muna muradin ganin cewar an cire mana takunkumin da aka ɗora mana ,tare da sake amincewa damu a matsayin wakiliyar kungiyar kasashen larabawa".

Da yake tabbatar da samun wasikar gwamnatin na Siriya, babban sakataren kungiyar kasashen larabawa Nabil al-Arabi ya bayyana cewar ta ƙunshi sabbin bukatu. Arabi yace sun tuntuɓi ministocin harkokin waje dangane da wasikar, kuma yanzu haka ana tattaunawa.

Damaskus dai ta ƙi rattaba hannu, dangane da cewar ka'idojin yarjejeniyar ya rage mata 'yanci, wanda hakan ne ya jagoranci kungiyar kasashen larabawan kakaba mata jerin takunkumi a ranar 27 ga watan Nuwamba, wadanda suka hadar da tsayar da dukkan wata hulda da Damaskus da babban Bankinta na kasa.

Tuni dai ƙungiyar tarayyar Turai da Amurka suka sanya mata takunkumi, kana a ranar juma'ar data gabata ne hukumar kare hakkin jama'a ta Majalisar Ɗunkin Duniya ta gabatar da kudurin yin Allah wadan ci gaban cin zarafin jama'a, da hana su 'yancin walwala a ɓangaren gwamnatin Siriya.

Duk da amincewar Damaskus na barin masu sa ido shiga kasar, 'yan adawar kasar sun bayyana shakkunsu. Ɗan jarida kuma marubuci Louay Hussein ya jima yana adawa da shugaba Bashar al-Assad, kuma yana ɗaya daga cikin waɗanda suka shirya taron adawa na ƙasa na farko a Siriya.

Syrien Demonstration gegen Präsident Bashar Assad in Damaskus Vorort
Masu boren adawaHoto: dapd

" Gwamnatin Siriya na daukar dukkan matakai na ganin cewar bata darajawa bukatun ƙungiyar ƙasashen larabawa ba. Wadanda suke mulki basa muradin kawo karshen wannan rikici".

Suma kungiyoyin kare hakkin jama'a na ci gaba da dasa ayar tambaya bisa ga la'akari da halin da ake ciki na ci gaban ruruwar wutar rikici a kasar ta Siriya. Ƙungiyar kare hakkin bil'adama ta Siriya dake da matsugunninta a kasar Britaniya ta ruwaito cewar an jibge gawarwakin fararen hula masu bore 34, a garin Al-Zahra dake da magoya bayan gwamnati. Ƙungiyar ta ce jami'an tsaron sun sace 'yan adawan ne daga garuruwa daban-daban na birnin Homs, wanda ke karkashin mamayen jami'an tsaron gwamnati tsawon watannin biyu da suka gabata.

A hannu guda kuma, sojojin da suka ɓalle daga rundunar gwamnati sun kashe jami'ai 4 daga cikin na gwamnati.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Yahouza Sadissou Madobi