1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Siriya ta dauki alhakin faduwar jirgin Turkiyya

June 23, 2012

Sojojin Siriya sun ce sun harbo jirgin ne bayan da ya ratsa iyakan kasar da Tukiyya ba tare da an gane mafarin shi ba.

https://p.dw.com/p/15KFg
A Turkish Air Force F-4 war plane fires during a military exercise in Izmir, in this May 26, 2010 file photo. Turkey lost a F-4 warplane, similar to the one pictured, over the Mediterranean on June 22, 2012, but Turkish Prime Minister Tayyip Erdogan said in his first public comments, he could not say whether the plane had crashed or been shot down. REUTERS/ Osman Orsal/Files (TURKEY - Tags: MILITARY CIVIL UNREST TRANSPORT POLITICS)
Hoto: REUTERS

Siriya ta bada tabbacin cewa, ita ce ta kabo jirgin saman yakin Turkiya da ya ketara sararin samaniyar yankinta ran juma'a, abun da ya janyo wani sabon rikici tsakanin kasashen biyu. Frime Ministan Turkiyya Rajeb Tayyib Erdowan ya ce kasarsa zata sanar da matsayinta nan ba da dadewa ba, ta kuma dauki duk matakan da suka dace da zarrar aka kammla fayyace wannan batu.

Wani mai magana da yawun dakarun sojin Siriya ya fadawa kamfanin dillancin labarun kasar na SANA cewa jirgin ya bude wuta ne kan wasu wadanda ba'a riga an gano ko su wanene ba, da shigarsa yankin Siriyar. Majalisar Dinkin Duniya dai tana sanya ido kan wannan rikici.

To sai dai wannan na zuwa ne bayan da wasu 'yan uwa hudu biyu a rundunar sojin Siriyar, daga cikin su masu rike da mukamin birgadiya Janar da kuma Kanar biyu suka sanar da cewa sun canza sheka a wani faifayin bidiyon da suka wallafa a yanar gizo.

Mawallafiya: Pinado Abdu Waba
Edita: Halima Balaraba Abbas