1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Siriya ta amince da shirin samar da zaman lafiya

March 27, 2012

Gwamnati a birnin Damaskus ta nuna amincewarta da shirin kawo ƙarshen zubar da jini a ƙasar ta Siriya da Kofi Annan ya gabatar.

https://p.dw.com/p/14SxO
Kofi Annan, joint special envoy for the United Nations and the Arab League, gestures during a news conference at Sheremetyevo International Airport outside Moscow, March 26, 2012. Annan said on Monday that the crisis in Syria "cannot drag on indefinitely" but that he could not set a deadline for a resolution after a year of bloodshed. REUTERS/Denis Sinyakov (RUSSIA - Tags: POLITICS CIVIL UNREST)
Kofi Annan dai na rangadin ƙasashen duniya akan rikicin SiriyaHoto: Reuters

Wakili na musamman na Majalisar Ɗinkin Duniya da ƙungiyar ƙasashen Larabawa Kofi Annan ya gana da wakilan ma'aikatar harkokin wajen China da firaminista Wen Jiabao akan rikicin ƙasar Siriya. Tsohon Sakatare janar ɗin na Majalisar Ɗinkin Duniya ya je Chinar ne don neman goyon bayan ƙasar ga shirinsa na kawo ƙarshen rikicin Siriya, wadda ta shafe fiye da shekara guda tana fama da rigingimu. Annan ya na birnin Beijing ne bayan tattaunawar da yayi da hukumomin Rasha a birnin Mosko. Wani kakakinsa ya ce gwamnatin Siriya ta amince da shirin Annan ɗin mai rukunnai guda shida da nufin kawo ƙarshen zubar da jini. Shirin ya tanadi janyewar dakarun gwamnati daga cibiyoyin 'yan adawa da ba wa 'yan agaji izinin shiga yankunan da ake yaƙi, sako firsinoni tare da kuma ba wa 'yan ƙasar damar samun taimakon jin ƙai. Halin da ake ciki a Siriyar ne ya mamaye zauren taron ƙolin ƙasashen Larabawa da ake yi a wannan Talata a birnin Bagadaza na ƙasar Iraqi.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Usman Shehu Usman