Siriya na fuskantar matsin lamba
September 6, 2012Ministocin harkokin waje na ƙungiyar ƙasashen larabawa da ke ci gaba da gudanar da taro a birnin Alƙahira na ƙasar Masar;sun yi Allah wadai da abin da suka kira kisan gila da gwamnatin Bashar Al Assad ke aiwatar wa akan jama'a,haka kuma ministocin sun buƙaci gwamnatin ta Siriya da ta dakatar da ta'adin.
Shugaban ƙasar Masar Mohamed Mursi mai masabkin baƙin wanda ya ce ya zama tilas gwamanatin Bashar Al Assad ta yi marabus ya ƙara da cewar.Ya ce ''ba zamu iya kauda ido ba akan abin da ke faruwa a Siriya, ya kammata mu samu hanyoyin warwware rikicin da gauggawa''.Ƙasashen dai na larabawa sun gargaɗi kwamitin sulhu na MDD da ya gurfana da hukumomin Siriya da na ƙungiyoyin yan gani kashe ni na gwamnati ,a gaban koutun duniya waɗanda ke da hannu a cikin kisan ƙare dangin na Siriya.
Mawallafi: Abdourahamane Hassane
Edita : Halima Balaraba Abbas