Siriya na fuskantar barazanar ƙarancin abinci
March 14, 2012Hukumomin na ayyukan gona da na cimmaka na Majalisar Ɗinkin Duniya na FAO da na PAM waɗanda ke da cibiyoyi a birnin Rome na ƙasar Italiya na ƙaddamar da ayyukan agajin na gaggauwa ga mutane kusan dubu dari a Siriyar sakamakon tashin hankalin da ake fama da shi wanda kawo yanzu Majallisar Ɗinkin Duniya ta ce mutane kusan dubu bakwai suka mutu
Hukumar ta ce yankunan da lamarin ya fi ƙamari su ne garuruwan Homs da Hama da Dara'a da kuma Idelb inda wasu duban jama'a suka ficce daga garuruwan,hukumar ta FAO ta ambato wani ofishin ƙididiga na Siriya na mai cewa tsananin hahauwar frashin kayan abinci da ake fuskanta da kuma ƙarancin man feutir ya sa kuɗin sufirin na mota ya ƙaru.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Zainab Mohammed Abubakar