1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zur Debatte im UN-Menschenrechtsrat

February 29, 2012

Duk da ƙoƙarin Rasha na kare gwamnatin Assad amma a yanzu haka a bayyane yake cewa yana da mahimmanci a ɗauki matakin samun mafita daga rikicin Siriya.

https://p.dw.com/p/14C3X
U.N. High Commissioner for Human Rights Navi Pillay addresses the 19th session of the Human Rights Council at the United Nations in Geneva February 27, 2012. REUTERS/Denis Balibouse (SWITZERLAND - Tags: POLITICS HEADSHOT)
Navi Pillay Kwamishanar hukumar kula da hakkin bil adama ta MDDHoto: Reuters

A baya an sha kwatanta hukumar kare haƙin bil Adama ta Majalisar Ɗinkin Duniya a matsayin wani kare mai yawan haushi amma ba ya cizo, ko kuma wani dandalin da wakilan ƙasashen dake fatali da haƙin ɗan Adam ke yaɗa farfagandarsu. Saboda haka muhauwarar da hukumar ke yi yanzu akan ƙasar Siriya, wata dama ce a gareta ta wanke kanta daga wannan zargin, kamar yadda Daniel Scheschkewtz ya rubuta a cikin wannan sharhin.

Ƙoƙarin tsagaita wuta da kai kayayyakin agaji a Siriya

Hukumar ta kare haƙin ɗan Adam ka iya ceto kanta daga mawuyacin halin da aka shiga a kwanakin baya ta hanyar zartas da ƙuduri mai tsauri da zai yi tir da mummunan keta haƙin bil Adaman da gwamnatin Bashar al-Assad ke yi, sannan ta nemi marikitan ƙasar ta Siriya da su tsagaita buɗe wuta.

Irin wannan tsagaita wuta za ta bawa ƙungiyar agaji ta Red Cross damar kai taimakon gaggawa ga mutanen dake a biranen da ake yaƙi a cikinsu.

Bai kamata ƙasashe 47 membobi a hukumar su biye wa Rasha ba, wadda jim kaɗan da fara taron ta nuna goyon baya ga gwamnatin Siriya. Mosko dai ta amince ta shiga muhauwarar ne bisa sharaɗin cewa a ƙarshe ba za a zartas da wani ƙuduri ba, amma ta manta cewa saɓanin kwamitin sulhu, a hukumar ta kare haƙin bil Adama babu damar hawa kujerar naƙi.

Duk da cewa ba dole ne ƙasashen duniya su yi aiki da ƙudurin hukumar ba, amma amincewa da shi wata kyakkyawar alama ce. Jami'ar kula da harkokin ƙetare ta ƙungiyar EU Catherine Ashton ta ce yawan mutane suka rasu tun bayan ɓarkewar bore a Siriya kimanin shekara guda ya kai 8000. A kwanakin nan yawansu na ƙaruwa musamman fararen hula da ake wa kisan ƙare dangi a kusa da birnin Homs dake zama cibiyar 'yan tawaye.

Overview of the U.N. Human Rights Council during the emergency debate on human rights and humanitarian situation in Syria, at the United Nations in Geneva February 28, 2012. Syria called on Tuesday for countries to stop "inciting sectarianism and providing arms" to opposition forces in the country, and charged that sanctions imposed by some countries were preventing Damascus from buying medicines and fuel. REUTERS/Denis Balibouse (SWITZERLAND - Tags: POLITICS)
Hoto: Reuters

Duk wani ƙuduri na hukumar kare haƙin bil Adama ka iya sa gwamnatin Siriya amincewa da buɗe hanyoyi da za su bawa ƙungiyar Red Cross damar kai wa ga waɗanda suka jikata tare da taimakawa mutane a yankunan da ake bata kashi. A nan dai Rasha ta yi alƙawarin yin amfani da angizonta akan gwamnatin Siriya.

Yunƙurin samarwa Assad damar ƙauracewa zuwa ƙetare

Yayin da a birnin Geneva ake ƙoƙarin samun mafita a diplomasiyance, a bayan fage ana wani yunƙuri na ba wa shugaba Assad da iyalinsa damar yin ƙaura wata ƙasa ta ƙetare ba tare da ya gurfana gaban kotun duniya ba, muddin ya sauka daga karagar mulki, matakin da 'yan diplomasiyan yamma ke goya wa baya musamman don kauce wa wani dogon yaƙin basasa a Siriya. Wataƙila wannan shi ne aikin da sabon mai shiga tsakani na Majalisar Ɗinkin Duniya Kofi Annan zai yi, wato yi wa Assad wannan tayi. Irin wannan dabarar aka ɗauka kan tsohon shugaban Yemen kuma ta yi nasara.

Bisa la'akari da ta'asar da gwamnatin Siriya ta yi, ba wa ɗan kama karya damar ficewa daga ƙasar ka iya zama maslaha ta biyu mafi kyau, domin kawo ƙarshen zubar da jinin bayin Allah.

Mawallafi: Daniel Scheschkewitz/Mohammad Nasiru Awal
Edita: Usman Shehu Usman