Siriya na ci-gaba da yin luguden wuta akan 'yan adawa
April 8, 2012Akalla mutane fiye da dari daya ne aka bada rahoton sun rasa rayukansu a sassan kasar Siriya a jiya Asabar wadanda suka hada da fararen hula 86 a cigaba da barin wutar da sojin gwamnatin ke yi akan 'yan adawa. Jami'an sa ido na kasa da kasa sun ruwaito cewa dakarun gwamnatin Siriya sun zafafa kai farmaki akan 'yan adawa gabanin wa'adin tsagaita wuta da kuma janyewa wanda zai cika a ranar Talata mai zuwa. Farmakin na cigaba da gudana a daidai lokacin da sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-Moon a baya-bayan nan ya soki gwamnatin ta Damascus da zafafa kai hare hare, lamarin da yace ya sabawa sharadin kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya na tsagaita wuta. Majalisar Dinkin Duniyar ta yi kiyasin cewa mutane fiye da 9,000 ne aka kashe a Siriyan tun bayan barkewar bore shekara guda da ta wuce.
Mawallafi: Abdullahi Tanko Bala
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe