1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Siriya: Mutane da dama sun mutu a wani harin roka

Gazali Abdou Tasawa
March 21, 2018

A kasar Siriya mutane 35 sun hallaka sakamakon wani harbin roka da ake zargin mayakan 'yan tawayen kasar ne suka kai shi kan kasuwar unguwar Jaramana da ke a gabashin babban birnin kasar.

https://p.dw.com/p/2ufZq
Syrien Ost Ghouta Zerstörung nach Luftangriff
Hoto: picture-alliance/AA/M. Abu Taim

 

Kamfanin dillancin labaran kasar na Sana ya ruwaito cewa akasarin mutanen da suka mutu a cikin harin wanda aka kai kasuwar da ke kusa da wani shingen bincike na sojojin kasar, fararan hula ne. Wasu shaidun gani da ido sun bayyana cewa harin ya ritsa da yara kanana da dama.

Wannan hari ya zo ne lokacin da sojojin gwamnatin Shugaba Bashar al-Assad masu samun goyon bayan kasar Rasha ke ci gaba da lugudan wuta a birnin Goutha da ke zama tungar karshe ta 'yan tawayen kasar ta Siriya inda fararan hula sama da dubu daya da 450 suka halaka a wata daya na wannan farmaki.