1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Siriya: Masu aikin bincike sun isa Douma

Gazali Abdou Tasawa
April 17, 2018

Tawagar kwararru na hukumar yaki da yaduwar makamai masu guba ta isa a wannan talata a birnin Douma na Siriya inda za ta gudanar da bincike kan zargin amfani da makami mai guba kan 'yan tawaye a birnin.

https://p.dw.com/p/2wDTC
Syrien - Giftgasangriff auf Duma
Hoto: picture alliance/XinHua/dpa/A. Safarjalani

Tawagar kwararru na hukumar yaki da yaduwar makamai masu guba ta isa a wannan talata a birnin Douma na Siriya inda za ta gudanar da bincike kan zargin da wasu manyan kasashen duniya ke yi wa kasar ta Siriya na yin amfani da makami mai guba kan 'yan tawayen kasar a birnin Douma na yankin gabashin Ghouta. 

Kamfanin dillancin labaran kasar ta Siriya na Sana ya shaida zuwan tawagar kwararrun garin na Douma inda ake zargin mutane sama da 40 sun halaka bayan da suka shaki iskar gubar a ranar bakwai ga watan Aprilun da muke ciki. 

Gwamnatocin kasashen Siriya da Rasha dai sun musanta amfani da makamin mai gubar a wannan gari,suna masu zargin 'yan tawayen Siriyar da shirya wannan makarkashiya da nufin shafa wa gwamnatin Siriyar kashin kaji. 

Sai dai kuma tuni jakada Amirka a hukumar yaki da yaduwar makaman masu guba Ken Ward ya ce da wuya binciken ya iya gano wani abu domin akwai yiwuwar Rasha ta ziyarci wurin da za a gudanar da binciken ta badda duk wasu alamu da ka iya tabbatar da afkuwar harin makamin mai guba.