1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Angela Merkel ta nemi a gaggauta dakatar da fada

Ramatu Garba Baba
October 14, 2019

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta ce illolin da sabon fadan Siriya zai haddasa na da yawan gaske saboda haka a gaggauta kawo karshensa.

https://p.dw.com/p/3REQV
Türkei Vierer-Gipfeltreffen in Istanbul l Thema Syrien
Hoto: picture-alliance/AA/c. Oksuz

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta nemi a gaggauta dakatar da fadan da ake a kasar Siriya, a tattaunawar da ta yi ta wayar tarho da Shugaba Recep Tayyip Erdogan da maraicen ranar Lahadi, ta ja hankalinsa don gani ya dauki matakin ba tare da bata lokaci ba.

Merkel ta tabo illolin da za a fuskanta in har fadan ya ci gaba da suka hada da kaurar jama'a da jefa yankin cikin sabon tashin hankali da kuma farfado da ayyukan mayakan IS. Kawo yanzu mayakan Kungiyar da ke da'awar jihadi fiye da dari bakwai ne suka tsere daga gidajen yari bayan da rundunar yakin Turkiyya ta afkawa arewacin kasar ta Siriya don yakar 'yan tawayen Kurdawa.

A wani lokaci a wannan Litinin, ministoci mambobin kasashen Kungiyar Tarayyar Turai EU za su yi zama kan matakin gwamnatin Ankaran, akwai yiyuwar garkama mata takunkumai na tattalin arziki tare da haramcin mallakar makamai.