1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Siriya: Birnin Raqa na shirin kubuce wa kungiyar IS

Gazali Abdou Tasawa MNA
September 20, 2017

Rundunar kawancen kungiyoyin tawayen kasar masu samun goyon bayan Amirka a cikin yaki da kungiyar IS ta yi nasarar karbe iko da sama da kashi 90 cikin 100 na birnin Raqa daga hannu kungiyar.

https://p.dw.com/p/2kO85
Syrien Rakka
Hoto: Getty Images/D.Souleiman


Rahotanni daga Siriya na cewa rundunar kawancen kungiyoyin tawayen kasar masu samun goyon bayan Amirka a cikin yaki da kungiyar IS ta yi nasarar karbe iko da sama da kashi 90 cikin 100 na birnin Raqa daga hannu kungiyar a wannan Laraba.

Kungiyar masu sa ido kan yakin kasar ta Siriya ta OSDH ta shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa wasu jerin hare-hare ta sama da jiragen yakin kawancen suka zafafa a kwanaki biyu na baya-bayan nan sun tilasta wa mayakan kungiyar ta IS ficewa daga cikin akalla unguwannin birnin biyar.

Sai dai kuma ta ce mayakan na IS na ci gaba da jan daga a wasu unguwannin tsakiyar birnin, inda suke rike da wasu manya-manyan gine-ginen gwamnati da suka hada da tsohuwar hedkwatar gwamnan birnin da kuma tsohuwar cibiyar leken asirin gwamnatin kasar ta Siriya.