1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Siriya: An kori 'yan IS daga Baghouz

Ahmed Salisu
March 23, 2019

Dakarun Kurdawa na Syrian Democratic Force (SDF) da ke samun goyon bayan Amirka sun ce sun samu nasarar korar mayakan Kungiyar IS daga tungarsu ta karshe a kauyen nan na Baghouz da ke gabashin kasar.

https://p.dw.com/p/3FZCM
Syrien Angriff auf IS Stellungen in Baghouz
Hoto: Getty Images/AFP/D. Souleiman

Dakarun suka ce bayan shafe makonni suna barin wuta kan 'yan IS din, a yau sun samu nasara karbe iko da Baghouz. Mai magana da yawun dakarun na Kurdawa Mustafa Bali shi ne ya tabbatar da wannan labari a wani sako da ya sanya a shafinsa na Twitter.

Da dama dai na ganin wannan shi ne yunkuri na karshe na karya kashin bayan kungiyar ta IS da ma kawo karshen mamayar da suka yi a Siriya din da kuma yunkurinsu na girka daular Islama.

Ya zuwa yanzu dai ba wani martani da aka samu daga 'yan kungiyar ta IS kan wannan batu sannan ba wani tartibin labari da aka samu game da halin da shugaban IS din Abubakar al-Baghdadi ke ciki.