Shugabar taimakon jin kai ta Majalisar Dinkin Duniya ta isa Siriya
March 7, 2012Shugabar hukumar taimakon jin kai ta Majalisar Dinkin Duniya Valerie Amos ta isa kasar Siriya a ranar Larabar nan domin yin kira ga gwamnatin kasar ta bada damar shigar da kayan agaji a biranen da tarzoma ta yiwa kaca-kaca. Valerie Amos wadda ta sauka birnin Damascus za ta tattauna da shugaba Bashar al-Assad. A ganawar da ta yi da Ministan harkokin wajen Siriyan Walid al-Mualem ya tabbatar mata cewa gwamnati za ta bada cikakken hadin kai.
A jiya manyan kasashe biyar masu kujarar dundundun a kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya sun gudanar da taro domin karin matsin lamba akan gwamnatin Siriya ta kawo karshen luguden wutar da take yi.
A waje guda kuma jakadan kasar Sin na shirin tattauna wani jadawali mai kudirori shida da Ministan harkokin wajen Siriya Walid Mu'alem domin kawo karshen rikicin. Ita ma kasar Rasha ta sake nanata kira ga gwamnati da yan tawayen Siriyan su gaggauta dakatar da fada.
Mawallafi: Abdullahi Tanko Bala
Edita: Saleh Umar Saleh