1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugabannin Yammacin Afirka sun gana kan tarzoma

Zulaiha Abubakar MNA
September 14, 2019

Shugabannin kasashen Yammacin sun dauki alwashin kawo karshen tsattsauran ra'ayin addini da ayyukan tarzoma da suka addabi yankin.

https://p.dw.com/p/3PcYd
Mauretanien G5 Sahel Taskforce
Hoto: Getty Images/AFP/T. Samson

Rahotanni daga Ouagadougou babban birnin kasar Burkina Faso sun bayyana yadda shugabannin kasashen Afirka 15 na kungiyar ECOWAS suka gudanar da taro don kawo karshen akidar tsattsauran ra'ayin addini da ta bazu a yankin da kuma muhimmancin rundunar tsaron hadaka ta G5 Sahel.

Shugabanni daga kasashen Yammacin Afirka sun jima suna gargadi game da yadda ayyukan ta'addancin da suka yi kakagida a Burkina Faso ke barazana ga yankin gaba daya bayan sun bukaci kasashen sun taimaka wa dakarun kungiyar G5 Sahel domin aikinsu ya fadada.

Yayin taron das uka gudanar a birnin Ouagadougou, ministan harkokin cikin gida daga jamhuriyar Nijar ya ja hankalin mahalarta taron game da karin kayan aiki da kudade don magance ta'addanci a Afirka.

Mazauna yankin arewacin Burkina Faso na fuskantar hare-haren kungiyoyin ta'adda daga iyakokin kasashen Mali da Nijar.

Rundunar tsaron ta G5 Sahel ta kunshi sojoji daga kasashen Chadi da Moritaniya da Mali da Nijar da kuma Burkina Faso mai masaukin baki.