Nijar da Mali da Burkina Faso na taro kan makomarsu
July 6, 2024
A karon farko, kasashen Nijar da Mali da kuma Burkina Faso da suka kwace mulki da tsinin bindiga daga hannun farar hula na gudanar da taron koli a karkashin kungiyar kawance ta AES.
Shugabannin sun kafa kungiyar kawancen yankin Sahel wato AES bayan fice wa daga ECOWAS sakamakon dakatar da su daga harkokin kungiyar. Dama dai kasashen sun yanke alaka da tsohuwar uwargijiyarsu Faransa, inda suka karkata alakarsu da kasar Rasha.
Karin bayani: Shugaban Nijar na ziyarar aiki a Mali da Burkina Faso
Fadar shugaban kasa ta Burkina Faso ta ce, batun yaki da ta'addanci da kuma karfafa hadin gwiwa a tsakanin kasashen su ne batutuwan da za su mamaye zauren tattaunawarsu. Kasashen Nijar da Mali da kuma Burkina Faso sun sha fama da matsalolin kungiyoyin da ke gwagwarmaya da makamai a kan iyakarsu wanda ya yi sanadin rayukan dakarun soji da kuma fararen hula da dama.
A gefe guda, shugabannin kungiyar ECOWAS za su gudanar da taron koli a Najeriya a ranar Lahadi.