1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugabannin jam'iyar dake mulki a Masar sun yi murabus

February 5, 2011

Masu adawa da mulkin shugaba Hosni Mubarak na Masar a fadin ƙasar sun ce ba za su dakatar da zanga-zanga ba har sai shugaban ya sauka daga kan muƙaminsa.

https://p.dw.com/p/10BUA
Za a ci gaba da zaman dirshan har sai an ga abin da ya turewa Buzu naɗiHoto: AP

A dangane da zanga-zangar adawa da gwamnatin Masar da ake ci gaba da yi, dukkan shugabannin jam'iyar dake mulki a ƙasar sun yi murabus daga muƙamansu. Gidan telebijin Al-Arabiya da ya ba da wannan labarin ya ce wannan matakin ya biyo bayan wata tattaunawa ce da ta gudana a fadar shugaban ƙasa. Shi ma ɗan shugaban Hosni Mubarak wato Gamal Mubarak ya yi murabus daga kwamitin zartaswar jam'iyar abin da ke zaman cikamakin murabus ɗin dukkannen shugabannin jam'iyar. Yanzu haka dai an naɗa Hossam Badrawi a matsayin sabon babban sakataren jam'iyar. Shi dai Badrawi na zama wani mai sassaucin ra'ayi dake da kyakkyawar alaƙa da 'yan adawar ƙasar ta Masar.

A wannan Asabar ma dake zama rana ta 12 a jere a boren da 'yan adawa ke yi a ƙasar ta Masar, dubun dubatan mutane sun hallara a dandanlin Tahrir dake birnin Alƙahira suna kira ga shugaba Mubarak da yayi murabus nan take daga muƙamin shugaban ƙasar. Wani rahoto da jaridar New York Times ta rawaito na nuni da cewa a Masar ana tunanin turo Mubarak zuwa Jamus domin duba lafiyarsa kamar yadda aka saba yi akai-akai ko kuma a kai shi wurin shaƙatawa nan na Sharm el-Sheikh. Ta haka za a iya kafa wata gwamnatin wucin gadi ƙarƙashin jagorancin sabon mataimakin shugaban ƙasa Omar Suleiman, domin fara tattaunawa da 'yan adawa ba tare da Mubarak ɗin ya rasa muƙaminsa nan-take ba.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Usman Shehu Usman