Shugaban ƙasar Masar ya naɗa Firaminista
July 24, 2012Shugaban ƙasar Masar Mohammad Mursi ya naɗa Hisham Kandil ministan noma rani mai barin gado a matsayin saban Firaminista.Qandil mai shekaru 50 a duniya, injiniya ne ta fannin harkokin noma.Yayi karatu a jami'ar birnin Alƙahira da kuma Caroline ta Arewa a ƙasar Amurika.
Ya riƙe manyan muƙammai a ofishin ministan dake kula da noma kamin daga bisani ya zama minista.Tun lokacin yaƙin neman zaɓe shugaba Mohammad Mursi ya yi alƙwarin naɗa Firaminista da zai samu karɓuwa daga jama'a, wanda ya samu cikkakar shaida ta fannin kishin ƙasa da nuna adalci.
A kwanaki masu zuwa Hisham Kandil zai gabatar da ministoci, a yanzu jama'ar ƙasa ta zuba ido ta ga ko gwamntai za ta ƙunshi ɓangarori daban-daban na jama'ar ƙasa ko kuma membobin jam'iyar 'yan uwa muslumi za su kalkace ta.
Mawallafi:Yahouza Sadissou Madobi
Edita:Saleh Umar Saleh