1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An rantsar da shugaba Emmerson Mnangagwa

Zulaiha Abubakar
August 26, 2018

Rantsuwar na zuwa ne bayan babbar kotun kasar tayi fatali da bukatar jogaran adawa Nelson Chamisa kan soke zaben sakamakon rashin gamsuwar sa da yadda sakamakon zaben ya kassance .

https://p.dw.com/p/33nLl
Simbabwe Amtseinführung nach Präsidentenwahl
Hoto: Reuters/P. Bulawayo

Wannan dai shi ne karo na biyu da aka rantsar da shugaban kasa a Zimbabuwe bayan hambarar da gwamnatin shugaba Robert mugabe, jim kadan bayan rantsuwar. Shugaba Mnangagwa ya jaddada aniyarsa ta farfado da tattalin arzikin kasar da ya durkushe, tare da gayyatar 'yan jam'iyyar adawa kan su ba shi hadin kai don ganin dimukuradiyya ta zauna a kasar. Da yake mayar da martani kan wannan tayi jagoran adawa Nelson Chamisa ya ce shi ba za a yaudare shi ba bayan an zalince shi.