1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Zambiya ya sadaukar da albashi

May 11, 2022

Shugaba Hakainde Hichilema na kasar Zambiya ya bayyana sadaukar da albashinsa na kowani wata a bangaren illimin kasar da ma taimakon marasa galihu.

https://p.dw.com/p/4B8B1
Shugaba Hakainde Hichilema na kasar Zambiya lokacin da yake adawa
Shugaba Hakainde Hichilema na kasar ZambiyaHoto: picture alliance/dpa/AP

A Zambia, shugaba Hakainde Hichilema ya bayyana cewa zai sadaukar da albashinsa na kowani wata a bangaren illimin kasar da ma taimakon marasa galihu. Dama tun bayan karbar ragamar mulkin kasar watanni takwas da suka gabata, har kawo yanzu Shugaba Hichilema bai karbi albashinsa ba, lamarin da ke shan fassara iri-iri a kasar.

Tun bayan da ministan kudi na Zambia Situmbeko Musokotwane ya sanar da cewa har kawo yanu shugaban kasa Hakainde Hichilema baya karbar albashinsa ba, al'umma a kasar ke kallon labarin tamkar almara tare da dasa ayar tambaya kan dalilin da ya haifar da hakan, sai dai a hanzu Shugaba Hichilema ya fito karara ya bayyana aniyarsa ta sadaukar da albashin shi wajen ganin marasa galihu sun sami ingantaccen illimi. Shugaban kasar ya yi ikrarin cewa inganta rayuwar al'umma ya sanya a gaba ba karbar albashi ba. Wannan mataki na shugaban kasar dai ya haifar masa da karin farin jini a idon 'yan kasar kamar yadda Zelu Muntali ta bayyana.

Zambiya | Rantsar da Shugaba Hakainde Hichilema na kasar Zambiya
Shugaba Hakainde Hichilema na kasar ZambiyaHoto: Salim Dawood/AFP/Getty Images

To sai dai ga Emmaneuel Mbewe da ke zama ma'aikaci a kasar na ganin karamcin shugaban kasar ba zai yi tasiri ba saboda a cewarsa idan dambu ya yi yawa ba ya jin mai.

Mbewe dai na ganin ko baya ga samar da guraben aiki akwai bukatar shugaban ya daidaita darajar kudin kasa tare da saukaka wa mutane wahalhalu na rayuwa ta hanyar karya farashin kayayyaki. Ko da yake wasu na ganin rashin amsar albashi ba wani babban al'amari ba ne ga shugaban kasar saboda tarin dukuiyarsa da kuma hanyoyin kudaden shigarsa, to sai dai a ra'ayi irin nasu Davis Mando suna ganin hannu daya ba ya daukar jinka.

Shugaba Hichillema na daga cikin manyan attajiran 'yan kasuwan kasar, inda dukiyarsa ta kai kimanin dala miliyan 400. A kasar ta Zambiya dai dala 350 ne ke zama mafi karancin albashi.