1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Museveni

Suleiman Babayo ZMA
July 28, 2020

Jam'iyya mai mulkin kasar Yuganda, National Resistance Movement (NRM), ta zabi Shugaba Yoweri Museveni a matsayin dan takara a zaben shugaban kasa na shekara mai zuwa ta 2021.

https://p.dw.com/p/3g51W
Yoweri Museveni
Hoto: picture-alliance/dpa/A. Novoderezhkin

Jam'iyya mai mulkin kasar Yuganda, National Resistance Movement (NRM), ta zabi Shugaba Yoweri Museveni a matsayin dan takara a zaben shugaban kasa na shekara mai zuwa ta 2021, domin neman wa'adi na shida na mulkin kasar. Museveni dan shekaru 75 da haihuwa tsohon dan tawaye wanda ya kwace madafun iko tun shekarar 1986 fiye da shekaru 30 da suka gabata, ya sauya kundin tsarin mulki tare da cire wa'adin da shugaban kasa zai yi tun shekara ta 2005.

A shekara ta 2019 kotun tsarin mulki ta tabbatar da kawar da shekaru da a baya aka hana dan ya wuce idan zai nemi mukamun shugaban kasa. Shugaba Yoweri Museveni zai fuskanci babban mai adawa da shi Bobi Wine mawakin da ya rikide ya zama dan siyasa a zaben kasra ta Yuganda da ke yankin gabashin Afirka.