Shugaban 'yan sanda na Ferguson ya yi marabus
March 12, 2015Talla
Shugaban 'yan sanda na Ferguson da ke cikin jihar Missouri a Amirka ya yi marabus.inda kwanan baya a garin da ke cikin jihar Missouri jama'a suka yi ta yin bore.
Bayan kisan wani matashi baƙar fata Michael Brown da wani ɗan sandar farar fata ya yi a cikin watan Agustan da ya gabata. wannan marabus na Thomas Jackson ya zo ne bayan wani sakamakon bincike da ofishin minista shari' a na Amirka ya bayyana kan cewar 'yan sandar na cin zarafin baƙar fata a Amirka.