1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arzikiJamus

Matakin shimfina bututun gasn na Turai ya janyo cece-kuce

Abdoulaye Mamane Amadou SB
August 22, 2021

Shugaba Volodymyr Zelensky na Ukraine ya caccaki matakin kewaye Ukraine idan aka shimfida bututun Gaz na Nord Stream 2, lokacin ganawa da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel.

https://p.dw.com/p/3zM3E
Ukraine | Angela Merkel und Wolodymyr Selenskyj
Hoto: Ukrainian Presidential Press Office/AP/picture alliance

Shugaba Volodymyr Zelensky na Ukraine ya caccaki shirin nan na shimfida bututun iskar gaz Nord Stream 2 da ke tsakanin Rasha da tarayyar Jamus, tare da bayyana shi a matsayin wani makami na siyasa da gwmanatin Rasha ke amfani da shi.

M. Zelensk da ke jawabi a yayin wata ziyarar aiki da shugabar gwamnatin Jamus Anglea Merkel ke yi a Ukraine, ya ce kasarsa za ta yi asarar dala miliyan dubu daya da rabi idan har aka shimfida bututun ta karkashin tekun Baltik bayan ya kewaye Ukraine. Sai dai shugaba Merkel ta ce tuni aka cimma wata yarjajaniya da Amirka kan batun tsawaita kwantaragin layin bututun gaz din da ke bi ta Ukrai da ke shirin karewa a shekarar 2024 da ke tafe, baya ga hana Rasha fakewa da shimfida bututun iskar gaz din don cimma wata manufa ta siyasa. 

Merkel ta kuma ce wannan batun zai kasance daga cikin manyan batutuwan da sabuwar gwamnatin da za ta gajeta za ta ba kulawa, bayan ta kawo karshen mulkinta a wannan shekara.