1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Erdogan ya maka babban dan siyasar da ke adawa da shi a kotu

February 18, 2021

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya shigar da karar babban dan siyasar da ke adawa da shi a siyasar kasar.

https://p.dw.com/p/3pZRt
UN-Generalversammlung | Recep Tayyip Erdogan
Hoto: Ercin Top/AA/picture alliance

Erdogan ya zargi Shugaban jam'iyyar adawa Kemal Kilicdaroglu da bata masa suna a kan batun kisan da Turkiyya ta ce mayakan Kurdawa sun yi wa 'yan kasar su 13 a arewacin Iraqi a makon da ya gabata. 

Duk da cewa mayakan Kurdawan sun fito sun musanta zargin da Shugaba Erdogan ya yi musu amma maganar ta zama babban abin da 'yan siyasa ke tattaunawa a cikin Turkiyya, inda shi shugaban adawa Kemal ya zargi Erdogan da sakaci wurin kisan mutanen. Sai dai kuma a yanzu lauyoyin  Shugaba Erdogan sun ce suna bukatar dan adawar ya biya Erdogan kudin da suka kai Euro 60,000 a matsayin diyyar bata masa suna da ya yi.