1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Evgueni Prigojine ya isa kasar Belarus

June 28, 2023

Hukumomin Belarus sun ce shugaban kamfanin Wagner Yevgeny Prigozhin wanda ya yi yunkurin yi wa Putin tawaye ya isa Minsk babban birnin kasar a ranar Talata.

https://p.dw.com/p/4T952
Yevgeny Prigozhin
Hoto: AP/picture alliance

Shugaban kasar Belarus Alexander Lukashenko wanda ya yi nasarar kashe wuta tsakanin shugaban Wagner da fadar Kremlin, shi ne ya sanar da isowar ta Yevgeny Prigozhin a cikin wata hira da ya yi da gidan yada labaran kasar na Belta.

A daura guda kuma, a daidai lokacin da Prigozhin ya isa Belarus, Amurka ta ce ta dauki sabbin matakai na ladabtarwa a kan dakarunsa na Wagner da ke aiki a wasu kasashen nahiyar Afirka, amma ba tare da ta yi karin bayani kan matakan ba.

Daga nasa waje shi kuwa Fafaroma Francis, manzo na musanman ya aike i zuwa Moscow domin duba hanyoyin kawo karshen mamayar da Rasha ta kaddamar kan Ukraine yau sama shekara guda.