1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Najeriya ya nemi afuwar jakadun ƙasashen waje

January 18, 2012

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya nemi afuwar jakadun ƙasashen waje game da halin rashin jin daɗi da suka fuskanta a sakamakon yajin aikin gama gari da kuma zanga zangar da suka faru a ƙasar.

https://p.dw.com/p/13lBS
Nigeria / Goodluck Jonathan / Präsident
Shugaban Najeriya Goodluck JonathanHoto: AP

Shugaban ya shaidawa jakadun yayin wata walima a daren jiya cewa yana mai matuƙar jimamin halin da wasun su suka shiga a sakamakon matakin gwamnatin na sake fasalin harkokin mai da daidaita farashinsa wanda ya kai ga cire tallafin da gwamnatin ke bayarwa akan man. Mutane dai da dama sun rasu a zanga zangar adawa da ƙarin farashin man a faɗin ƙasar ciki har da wasu mutane biyu da 'yan sanda suka bindige har lahira, lamarin da ya ƙara haifar da zanga zangar ƙungiyoyin ƙwadago dana farar hula a sassan jihohin ƙasar. A ranar Litinin ɗin da ta wuce Jonathan ya sanar da rage farashin man zuwa Naira 97 akan kowace lita saɓanin Naira 141 da gwamnatin ta sanar tun da farko. Jami'an gwamnatin da masana tattalin arziki na baiyana cewa cire tallafin zai baiwa gwamnatin damar tsimin Dala biliyan takwas a kowace shekara domin gudanar da ayyukan raya ƙasa da cigaban al'uma. Al'umar Najeriyar miliyan 160 dai na rayuwa ne akan ƙasa da Dala biyu a rana.

Mawallafi: Abdullahi Tanko Bala
Edita: Umaru Aliyu