Shugaba IBK na Mali ya yi nassara a zaben kasar
August 16, 2018Shugaban mai ci na kasar ta Mali ya yi nasar ce a gaban abokin takararsa Soumeila Cisse na bangaran adawa, wanda ya samu kashi 32, 83 cikin 100. Hakan zai bawa shugaban da 'yan kasar ke kiran shi da sunan IBK damar yin wani sabon wa'adin mulki na biyu.
Da dama dai na kallon shugaba Boubakar Keita, wanda aka haifa a garin Koutiala da ke kudancin kasar ta Mali kusa da Burkina Faso, a matsayin mai kyauta, amma da saurin fushi da kuma nuna bangaranci, wanda a wa'adin mulkinsa na farko na shekara biyar, ya sauya firaminista har sau biyar, sannan daga cikin abokan takararsa 23 a zagayan farko na zaben, akwai da dama da suke tsaffin ministocinsa ne abin da ke nuni da yadda shugaban ke da wuyar sha'ani.
A wa'adin farko an zabi shugaban kasar ta Mali ne da kashi 77,6 cikin 100, amma kuma a cewar masu adawa da mulkinsa hakan bai sa shi yin wani abin azo a gani kan mahimman batutuwan da suka addabi 'yan kasar ta Mali ba.