1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban majalisar dokokin Rasha ya yi murabus

December 14, 2011

Bayan da jamiyar United Russia dake mulki ta yihasarar rinjayenta a majalisa . shugaban majalisar Boris Gryslov ya yi murabus

https://p.dw.com/p/13SuH
Members of pro-Kremlin youth movements gather at the Triumphal Square in downtown Moscow, Tuesday, Dec. 6, 2011. Police clashed Tuesday on a central Moscow square with demonstrators trying to hold a second day of protests against alleged vote fraud in Russia's parliamentary elections. Hundreds of police had blocked off Triumphal Square on Tuesday evening, then began chasing about 100 demonstrators, seizing some and throwing them harshly into police vehicles. (Foto:Sergey Ponomarev/AP/dapd)
Zanga-zangar nuna adawa da sakamakon zabe a RashaHoto: dapd

 A kasar Rasha  shugaban majalisar dokoki Boris Gryslov ya yi muabus bayan da jam'iyyar da ke mulki ta yi hasarar rinjaye da take da shi a zaben majalisar dokokin kasar . Gryslov ya ba da sanarwar murabus dinsa ne a shafin yanar gizo na jam'iyyar United Russia ba tare gwada dalilin da ya sa ya tsai da wannan shawara ba. Gryslov wanda a da ya rike mukamin ministan cikin gida na zama fitacen dan siyasar kasar da ya sauka daga mukaminsa  bayan da jam'iyyarsa ta yi asarar rinjayen da take da shi a zaben da ya gudana a ranar hudu ga Disamban 2011.  Gryslov dai shi ne na hannun damar fraiminista Vladimir Putin da ke jan ragamar jam'iyyar. Mataimakin shugaban gwamnati,   Alexander Schukov shine yanzu zai rike wannan mukami. Da kusan kashi 50 daga cikin dari kacal  ne aka bayyanar da jam'iyyar United Russia a matsyin wadda ta lashe zaben-inda hakan ke ma'anar nakasu na kashi 15 daga cikin dari idan aka kwatanta da zaben da ya gudana shekaru hudu da suka gabata. 'Yan adawar kasar ta Rasha dai sun yi zargin tafka magudi a zaben.

 Mawallafiya; Halima Balaraba Abbas
Edita: Usman Shehu Usman