1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kim Jong Un bai mutu ba

April 27, 2020

Bayanai daga kasar Koriya ta Kudu na cewa shugaban kasar Koriya ta Arewa Kim Jong Un na nan a raye bai mutu ba.

https://p.dw.com/p/3bSI9
Nordkorea Kim Jong-un Besuch Luftabwehr Stützpunkt
Hoto: picture-alliance/Yonhap

Wani mashawarci ga shugaban kasar Koriya ta Kudu ne ya tabbatar da haka, yana mai watsi da jita-jitar mutuwar Kim Jong Un  da ake ta yadawa.

Wata jaridar intanet ta Koriya ta Arewa ce dai ta fara fitar da labarin cewa matashin Shugaban kasa  Kim Jong Un yana nan rai kwakwai-mutu-kwawai bayan da aka yi masa aiki a zuciyarsa saboda tsananin shan taba da kuma teba da yake fama da ita. Daga bisani kuma akai ta yadawa a shafukan sada zumunta cewa  Kim Jong Un ya mutu a sakamakon wannan aiki  da aka yi masa.

Sai dai jami'an gwamnati sun musanta wannan labari a wata hira da suka yi da gidan talabijin na CNN.