1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaVietnam

Shugaban kasar Vietnam ya yi murabus

March 21, 2024

Majalisar dokokin kasar Vietnam ta amince da murabus din shugaban kasar, shekara guda bayan hawansa kan karagar mulkin wannan kasa da ke karkashin ikon masu ra'ayin gurguzu.

https://p.dw.com/p/4dxVn
Vietnam | Vo Van Thuong
Hoto: Nhac Nguyen/AFP/Getty Images

Murabus din shugaba Vo Van Thuong mai shekaru 53 a duniya na zuwa ne a daidai lokacin da kasar Vietnam ta fada cikin rikicin siyasa bayan ajiye aiki da magabacinsa ya yi tare da korar wadansu ministoci da shugabannin ma'aikatu kan zargin badakala da dukiyoyin gwamnati.

Tuni ma dai aka nada mataimakiyarsa Thi Anh Xuan a matsayin shugabar rikon kwarya, kafin a samu wanda zai maye gurbinsa kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada.

Shi dai Vo Van Thuong ya hau kan gadon mulkin kasar ta Vietnam ne a ranar biyu ga watan Maris na 2023 bayan murabus din ba-zata da magabacinsa Nguyen Xuan Phuc ya yi, inda ya yi alkawarin samar da sauye-sauye don sake saita tafiyar kasar.

Vietnam dai na fama da matsalar cin hanci da rashawa da ta babaibaye ma'aikatun gwamnati, lamarin da ke hana ruwa gudu wajen ci gaban kasar da a shekarun baya ta share lokaci mai tsawo tana yaki da Amurka.