1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban kasar Jamus ya yi kiran hadin kai

November 20, 2018

Shugaban kasar Jamus Frank-Walter Steinmeier ya jaddada bukatar hadin kan kasashe don samun ci gaba mai ma'ana a fadin duniya.

https://p.dw.com/p/38YdA
Bundespräsident Steinmeier in Südafrika
Hoto: picture-alliance/dpa/B. von Jutrczenka

Mr. Steinmeier wanda ya yi gargadi kan yadda wasu ke rikon tsananin ra'ayin kishin kasa, ya ce lallai ne kasashe su hada kai domin iya shawo kan manyan matsalolin da duniya ke fuskanta. 

Shugaban na Jamus ya nuna bukatar hakan ne a kasar Afirka ta Kudu inda yake ziyarar kwanaki uku.

A jawabin da ya gabatar a gidan adana tarihi na mulkin wariyar launin fata da ke birnin Johannesburg, Shugaba Steinmeier, ya ce kasancewar Jamus da Afirka ta Kudun mambobin kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, zai dace kasashen biyu su yi amfani da damar wajen aiki tare.

Afirka ta Kudun dai ita ce kadai kasar Afirka da ke cikin kasashe 20 masu karfin tattalin arziki a duniya.