1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyarar shugaban Jamus na farko a Masar cikin shekaru 20

Abdul-raheem Hassan
September 10, 2024

Frank-Walter Steinmeier zai yi kwanaki uku a birnin Alkahira, a wata ziyara irinta ta farko cikin shekaru 20 da wani shugaban kasar Jamus ya kai Masar. Ziyarar za ta inganta kasuwanci da batun sulhunta Isra'ila da Hamas.

https://p.dw.com/p/4kTlG
Shugaban kasar Jamus, Frank-Walter Steinmeier
Shugaban kasar Jamus, Frank-Walter SteinmeierHoto: Sebastian Gollnow/dpa/picture alliance

Baya ga batun inganta huldar kasuwanci tsakanin kasashen Masar da Jamus, a halin yanzu, gwamnatin Jamus ta zuba jari a kamfanoni 1,620 da ke aiki a duk sassan tattalin arzikin Masar. Wadannan kamfanoni suna ba da gudummawa ga sauya cibiyoyin fasaha zuwa tattalin arzikin Masar tare da samar wa dubban mutane ayyukan yi a fadin kasar.

Shugaba Steinmeier da Shugaba Abdel Fattah al-Sisi za su tattauna hanyar warware rikin Isra'ila da Gaza da ya jefa yankin Gabas ta tsakiya cikin rashin zaman lafiya. Dama dai Masa da Katar na kan gaba cikin kasashen da ke yunkurin shiga tsakanin Isra'ila da kungiyar Hamas don samar da yarjejeniyar tsagaita wuta.

Zijyarar Steinmeier na zuwa ne a dai-dai lokacin da 'yan fafutuka ke zargin gwamnatin Al-Sisi da takun siyasa irin na mulkin kama karya, Shuagban na Jamus Frank-Walter Steinmeier, zai kuma gana da kungiyoyin kare hakkin 'yan Adam da cibiyoyin siyasar kasar Jamus da ke Masar.