1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Jamus ya jaddada goyon bayan ga gwamnatin Habasha

Abdul-raheem Hassan SB
January 28, 2019

A ci gaba da ziyarar Shugaba Frank-Walter Steinmeier na Jamus a Afirka, lokacin ziyara a Habasha ya jaddada goyon bayan Jamus ga irin yunkurin farfado da tattalin arziki da zaman lafiya karkashin Firaminista Abiy Ahmed.

https://p.dw.com/p/3CKdb
Äthiopien Frank-Walter Steinmeier am Addis Ababa Bole International Flughafen
Hoto: picture-alliance/dpa/B. Pedersen

Shugaban kasar Jamus Frank-Walter Steinmeier, ya samu tarba irin ta girmamawa ta faretin soji a Adis Ababa babban birnin kasar Habasha. Shugabar kasar Habasha Sahle-Work Zewde ce ta marabci tawagar Steinmier bayan ganawarsa da firaminista Abiy Ahmed. To ko me ya banbanta a idanun Shugaba Steinmeier a wannan ziyarar bayan zuwansa kasar shekaru 6 baya a matsayin ministan harkokin wajen Jamus?

Äthiopien Addis Abeba Nationalpalast | Bundespräsient Frank-Walter Steinmeier & Sahle-Work Zewde, Präsident
Shugaba Frank-Walter Steinmeier na Jamus tare da Shugabar kasar Habasha Sahle-Work ZewdeHoto: Deutsche Botschaft in Äthiopien

Ziyarara Steinmeier a Habasha, ta kunshi ganawar jinjina ga firamista Abiy Ahmed, kan yunkurin farfado da martabar kasar ta kawo karshen fahimtar juna tsakanin kabilu, da ma warware takaddamar siyasar gaba a kasar. Ziyarar ta Steinmier ta ta samu rakiyar 'yan kasuwa daga kamfanin kera motocin VV da kamfanin Siemens, domin ganawa da 'yan kasuwar Habasha kan dangantakar kasuwancin tsakanin kasashen biyu. Sai dai manema labarai sun yi amfani da wannan dama ta jin inda aka kwana kan batun girka kamfanin VV da sauran kamfanonin Jamus a Habsha. Amma Shugaba Steinmeier ya bayyana matsalolin da ke hana ruwa gudu a dangantakar kasuwancin kasa da kasa.

Deutschland Bundespräsident Steinmeier zu Staatsbesuch in Äthiopien
Shugaba Frank-Walter Steinmeier na Jamus da Firaminista Abiy Ahmed na HabashaHoto: Office of the Prime Minister Ethiopia 

Abiy Ahmed mai shekaru 42, ya kaddamar da jerin sauye sauye a kasar Habasha, cikin har da yaki da cin hanci da 'yancin fadin albarkacin baki  hada da bude kofofi ga harkar kasuwaci da sauran aksasehn duniya domin tada komadar tattalin arzikin da ya shiga wani yanayi na rashin tabbas. firamistan ya kuma samu lambar yabo kan cimma yarjejeniyar zaman lafiya ta abokiyar hamayyar Habasha wato Iritriya tare da sako dubban fursunonin siyasa da ba da damar shiga tattaunawa da 'Yan adawa.