1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Jamus na ziyara a Afirka

February 23, 2020

A wannan Lahadi ce shugaban kasar Jamus Frank-Walter Steinmeier zai fara ziyarar aiki a nahiyar Afirka. Ziyarar ta kwanaki biyar ita ce ta hudu da yake yi a Afirka.

https://p.dw.com/p/3YE6p
Bundespräsident Steinmeier in Botsuana
Hoto: picture-alliance/dpa/B. von Jutrczenka

Da fari dai Shugaba Frank-Walter Steinmeier, zai fara ne da kasar Kenya inda zai yi kokarin karfafa dadaddiyar alakar da ke tsakanin kasar da Jamus.

Daga nan kuma sai kasar Sudan duk dai a wannan makon, inda zai kai goyon bayan Jamus kan sabon tsari na dimukuradiyya da kasar ta kama.

Wannan ne dai karo na hudu da shugaban na Jamus Steinmeire ke kai ziyara Afirka, cikin shekarunsa uku da ya yi kan karagar mulki.

Sai dai wannan ne karon farko da shugaban Jamus ke ziyarar aiki a Kenya.

A ranar Litinin ne kuma ganawa da sauran hidindimu za ta wakana tsakaninsa da jiga-jigan kasar ta Kenya.