1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Shugaban gwamnatin Jamus Scholz zai gana da shugaban Amurka

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
February 9, 2024

Haka zalika shugabannin biyu za su tattauna batun rincabewar rikicin Gabas ta Tsakiya, da ke fama da yakin Isra'ila da Hamas, sai hare-haren da Amurka ke kai wa 'yan tawayen Houthi na Yemen masu samun goyon bayan Iran

https://p.dw.com/p/4cED0
Hoto: Jonathan Ernst/Pool/REUTERS

Shugaban gwamnatin Jamus Olaf  Scholz zai gana da shugaban Amurka Joe Biden a juma'ar nan a birnin Washington, don tattauna hanyoyin da za su bi wajen tallafawa Ukraine da kayan yaki da kuma biliyoyin Daloli, domin ci gaba da kare kanta daga mamayar da Rasha ta yi mata.

Karin bayani:Rikice-rikicen duniya sun ja hankalin jawabin shugaban gwamnati Olaf Scholz, na shiga sabuwar shekara

Haka zalika shugabannin biyu za su tattauna batun rincabewar rikicin Gabas ta Tsakiya, da ke fama da yakin Isra'ila da kungiyar Hamas, sai hare-haren da Amurka ke kai wa 'yan tawayen Houthi na Yemen masu samun goyon bayan Iran.

Karin bayani:Matsayar Jamus a rikicin Isra'ila da Hamas

Bukatar da fadar White House ta mika wa majalisar dattijan Amurka ta agazawa Ukraine da Dala biliyan 60 ta gamu da cikas din kin amincewar majalisar, har zuwa wannan lokaci.