Shugaban Faransa Sarkozy ya naɗa sabuwar gwamnati
May 18, 2007Talla
Shugaban ƙasar Faransa Nicolas Sarkozy ya naɗa yan majalisar gudanarwar gwamnatin sa. Waɗanda aka naɗa sun haɗa da Francois Fillon a matsayin P/M, sai kuma Bernard Kouchner wanda ya sami matsayin Ministan harkokin waje. Sauran naɗe-naɗen sun haɗa da Tsohon P/M Alain Juppe wanda aka baiwa Ministan muhalli da kuma Jean-Louis Borloo a matsayin Ministan ƙwadago da tattalin arziki.