1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Chadi ya ziyarci Isra'ila

November 25, 2018

A karon farko tun bayan kafa kasar Isra'ila, shugaban kasar Chadi Idriss Deby, ya kai wa firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu wata ziyarar ba-zata a wannan Lahadi.

https://p.dw.com/p/38sxJ
Tschad Präsident Idriss Deby
Hoto: picture-alliance/AA/E. Gurun

Shugaba Idriss Debyn ne dai shugaba na farko daga kasashen tsakiyar Afirka da ya ziyarci Isra'ilar tun samuwarta a shekara ta 1948, ziyarar kuwa da ofishin Mr. Netanyahu ya ce ta tarihi ce.

A shekara ta 1972, Chadi wadda galibin al'umarta musulmi ne, ta yanke huldar diflomasiyya da Isra'ila.

Tun cikin shekara ta 2016 ne dai firaminitan na Isra'ila ya mike tsaye don ganin ya kyautata huldar kasarsa da kasashen nahiyar Afirka da dama, ciki har da Kenya da Yuganda da Ruwanda da kuma Habasha.

Isra'ilar ta kuma taba alkawarin taimaka wa kasashen Afirka da yaki da ta'addanci, musamman ta fuskar bayanan sirri.