1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaLatin Amurka

Shugaban Brazil ya nemi duniya ta magance sauyin yanayi

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
September 24, 2024

A bana dai an yi fama da ibtila'i a sassa daban-daban na duniya, har ma mutane da dama suka rasa rayukansu

https://p.dw.com/p/4l2ok
Hoto: Mike Segar/REUTERS

Shugaba Luiz Inácio Lula da Silva na Brazil, ya yi kira ga kasashen duniya da su ba da himma, wajen daukar matakan gaggawa domin magance matsalolin da sauyin yanayi ke haddasa wa, sakamakon yadda shekarar nan da muke ciki ta 2024 ta kasance mafi tsananin zafi da aka fuskanta a tarihi.

Karin bayani:Brazil ta toshe kafar sada zumunta na X

Mr Lula da Silva ya yi wannan kira ne lokacin da yake gabatar da jawabi a taron babban zauren Majalisar Dinkin Duniya na yau Talata a birnin New York din Amurka, yana mai cewar wutar dajin da kasarsa Brazil ta fuskanta a bana, ita ce mafi muni da suka gani a cikin shekaru 20, kuma ta jefa Brazil din cikin rudani da tashin hankali.

Karin bayani:Babu wanda ya tsira da rai a hatsarin jirgin sama a Brazil

A bana dai an yi fama da ibtila'i a sassa daban-daban na duniya, har ma mutane da dama suka rasa rayukansu, kama daga guguwa a yankin kasashen Caribbean da Asia, sai ambaliyar ruwa a nahiyar Afirka, yayin da a Turai kuma aka fuskanci saukar mamakon ruwan sama.