1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Shugaban Benin na kokarin lashe zabe a karo na biyu

April 12, 2021

Shugaban kasar Jamhuriyar Benin Patrice Talon ya shirya ayyana samun nasara bayan zaben shugaban kasa da aka yi a karshen mako da ke cike da takaddama.

https://p.dw.com/p/3rrDd
Benin Präsident Patrice Talon
Hoto: PIUS UTOMI EKPEI/AFP

Tun kafin hukumar zaben kasar ta fitar da kammalallen sakamakon zabe, masu adawa da shugaban sun fara zargin sa da murdiya ta hanyar kuntata wa jagororin adawa.

Shugaban na Benin dai na fuskantar wasu 'yan takara daga bangaren adawa guda biyu da ake ganin duk yadda za ta kaya ba za su iya kayar da shi ba. Sai dai a gabanin zaben an zargi Shugaba Talon da amfani da hukumomin kasar wurin tsame sunayen jiga-jigan adawar da ya ke tunanin za su kawo masa tarnaki a zaben.

A shekara ta 2016 ne dai aka fara zaben Shugaba Talon a matsayin shugaban kasar ta Jamhuriyar Benin, kuma a cikin kasar wasu na ganin ya taimaka wurin habbakar tattalin arzikin kasa.