1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

SHUGABAN BANKIN DUNIYA YA KAMMALA ZIYARARSA A NAHIYAR AFIRKA

YAHAYA AHMEDJune 20, 2005

Bayan ziyarar mako daya da ya kai a nahiyar Afirka, sabon shugaban bankin duniya, Paul Wolfowitz, ya nuna gamsuwarsa da irin ci gaban da ake samu a nahiyar, musamman a huskar yakan cin hanci da rashawa da kuma nuna kyakyawan halin tafiyad da harkokin mulki.

https://p.dw.com/p/BwUP
Sabon shugaban bankin duniya, Paul Wolfowitz.
Sabon shugaban bankin duniya, Paul Wolfowitz.Hoto: AP

A karshen ziyarar mako daya da ya kai a nahiyar Afirka, sabon shugaban bankin duniya, Paul Wolfowitz, ya bayyana cewa, kafarsa za ta fi ba da muhimmanci ne ga nahiyar Afirkan a cikin manufofinta. A nasa ganin dai, Wolfowitz ya ce nahiyar, ta kasance wani babban kalubale ne ga gamayyar kasa da kasa. Amma a shirye yake, ya tinkari wannan gagarumin aikin don iya shawo kansa. Kamata ya yi dai, a mataki na farko, bankin duniyar, ya kara mai da hankalinsa kan bukatun nahiyar, inji Wolfowitz:-

„A nawa ganin, babu makawa, sai mun kara yin la’akari da bukatun kasashe masu tasowan, idan da gaske ne muna son mu taimake su. Kalmar ma ta taimako ba ta dace ba a nan, saboda ma’ammala za mu yi tare da juna, wato batu ne da ya shafi abokan hulda.“

Ta hakan dai, shugaban na bankin duniya na son sanya alama ne ta inganta ma’ammala tsakanin kafarsa da shugabannin nahiyar da kuma wasu hukumominta kamarsu NEPAD, wato hukumar nan da aka kafa don kula da ci gaban nahiyar. daya daga cikin jigajigan hukumar ta NEPAD ne tsamo Afirka daga kangin talauci da ta dade tana ciki. A nan kuwa, mizanin da take aiki da shi ne, bayyanannun harkokin gwamnati, da kyakkyawan halin mulki da kuma dimukradiyya. Tun cikin `yan shekarun da suka wuce ne dai bankin na duniya, ya shiga sahun kasashen rukunin nan na G-8, a yarjejeniyar da suka cim ma da hukumar ta NEPAD.

Game da ababan da ya gano wa idanunsa a ziyarar, Wolfowitz ya bayyana cewa, shi da tawagarsa sun koyi darussa daga kurakuran da aka yi a da. A lal misali ya ce, babu wata kasar da za ta iya samun ci gaba mai dorewa, ba tare da tana ingantattun tituna da wasu muhimman gine-gine ba:-

„Inda matsalar ta fi tsamari ne a kasashen Ruwanda da Burkina Faso, wadanda ba su da gabar tekun kansu. A nan tabbas ne lafiyayyun tituna da hanyoyin sadarwa su kasance muhimman jigogin gwamnati, kamar dai a kasashe masu ci gaban arzikin masana’antu. A nan Amirka, muna kashe kimanin dola biliyan daya da digo 8 wajen samad da wadannan fasalolin. Hakan ma zai karu nan gaba.“

Babbar sukar da kasashen Afirkan ke yi wa bankin duniya dai, ita ce ta tsawon lokacin da ake dauka, kafin bankin ya amince da takardar neman rance. Wolfowitz dai ya dau alkawarin sake nazarin wannan lamarin.

Ya kuma nuna gamsuwarsa ga kudurin da ministocin kudi na kasashen G-8 din suka zartar, na yafe wa wasu kasashe masu tasowa, mafi fama da talauci basussukan da ake binsu:-

„A nan dai, akwai wasu basussukan da bai kamata ma a ba da su ba tun da farko, saboda ba a yi amfani da kudaden kamar yadda ya kamata ba. Watakila ba da tallafi a nan zai fi ma’ana da rance. Dalilin da ya sa kasashen ke ta tara dimbin yawan basussuka kuwa shi ne shugabanninsu na da, sun yi amfani da kudaden da suka ranton ne wajen azurta kansu. A nan ina nufi ne da yaduwar cin hanci da rasahawa, da rashin tafiyad da kyakyawan hali na mulki. Amma a halin yannzu, ana ta kara samun sabbin shugabanni a nahiyar Afirka, wadanda ke tinkarar wannan matsalar don warware ta. Sabili da haka ne kuwa, na kei amanna da jawabin shugaban Najeriya Obasanjo, wanda ya ce Afirka na farfadowa, akwai kuma ababa da dama da ke wakana a nahiyar. Ina fata dai, bankin duniya zai iya gaggauta wannan ci gaban da ake samu.“