1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban bankin duniya ya gargadi kasashen Turai

June 17, 2012

Kasashen Turai na bukatar gaggauta daukar matakin ceto kudin Euro domin daideta tattalin arzikinsu

https://p.dw.com/p/15Gk9
World Bank Group President Robert Zoellick speaks during a news conference at IMF/ World Bank Annual Meetings at IMF headquarters in Washington, on Saturday, Sept. 24, 2011. Global finance officials pledged Saturday to take bolder moves to confront a European debt crisis that threatens to plunge the world into another deep recession. But sharp disagreements about exactly what to do can't offer much reassurance to markets rocked by uncertainly in recent weeks. (ddp images/AP Photo/Jose Luis Magana)
Robert ZoellickHoto: AP

Shugaban bankin duniya, Robert Zoellick ya gargadi kasashen Turai game da yadda suke rikon sakainar kashi ga rikicin kudi. Robert Zoellick ya yi wannan kiran ne gabanin shiga taron kasashen G20 da za a fara a ranar Litinin a kasar Mexico. Zoellick ya ce kasashen Turai a ko da yaushe suna sako-sako wajen daukar matakin da ya dace domin ceto kudin euro. A cikin firar da jaridar "Der Spiegel" ta yi da shi Zoellick ya soki matakin babban bankin Turai na sake neman gabatar da sabon matsayin durkushewar bankuna domin samun karin lokaci. Ya ce yin hakan ba zai warware ainihin matsalar da ke akwai ba. Shugaban bankin na duniya ya ce kasashen Turai na bukatar gaggauta daukar mataki wajen tinkarar wannan matsala.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Umaru Aliyu