1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaba Trump zai gana da Shugaba Kim

Yusuf Bala Nayaya
September 21, 2018

Sakataren harkokin wajen Amirka Mike Pompeo ya bayyana a ranar Juma'a cewa yana cike da fatan za a sake zaman tattaunawa tsakanin Shugaba Donald Trump da takwaransa na Koriya ta Arewa Kim Jong Un.

https://p.dw.com/p/35JsP
Bildergalerie Kim Trump
Hoto: Reuters/J. Ernst

A cewar sakataren harkokin wajen na Amirka "nan ba da dewa ba" za a tattauna tsakanin shugabannin a kokarin da ake na ganin kasar da ke a mashigar teku ta yi watsi da makaminta na nukiliya.

Pompeo ya ce shi ma yana fatan ba da dadewa ba zai yi tafiya zuwa birnin na Pyongyang a kokari na dorawa kan wannan tattaunawa. Sakataren harkokin wajen na Amirka dai ya bayyana haka ne ga kafar yada labarai ta MSNBC.

Ya ce shugabannin ba da dadewa ba za su zauna don samun ci gaba kan wannan tattaunawa da ke zama mai amfani ga al'ummar duniya.