1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban adawar Girka ya buƙaci Papandreou ya yi murabus

November 6, 2011

A ganawar da ya yi da shugaban ƙasar Girka madugun 'yan adawa Antonis Samaras ya gitta sharaɗin murabus ɗin Papandreou sannan jam´iyarsa ta bada haɗin kai

https://p.dw.com/p/135vW
Antonis SamarasHoto: picture-alliance/dpa

Madugun 'yan adawar ƙasar Girka, Antonis Samaras ya jaddada cewar cilas, sai firaminista Georges Papandreou yayi murabus, kamin ya bada haɗin kai wajen kafa sabuwar gwamnati.

A jiya Georges Papandreou ya gana da shugaban ƙasa, kuma ya samu izinin girka wannan gwamnati.A yau shima madugun adawa ya gana da shugaban ƙasa, inda ya gabatar da buƙatar murabus ɗin Papandreou wadda ya ɗauka a matsayin babban sharaɗin jam´iyarsa na shiga sabuwar gwamnatin.

Idan dai ba a manta ba, a jawabin da ya yi ranar Juma´a a majalisar Dokoki Firaministan Girka ya yi watsi da batun shirya zaɓen.

Wannan taƙƙadamar siyasa na ƙara muzanta matsalolin kuɗi da ƙasar Girka ke fama da su.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi

Edita: Ahmad Tijani Lawal