1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaba Trump ya koma fagen yakin neman zabe

Binta Aliyu Zurmi
October 12, 2020

A wannan Litinin Shugaba Donald Trump na Amirka zai mayar da batun cutar Covid-19 sahun baya, inda ya koma fagen yakin neman zabe kwanaki 10 bayan da aka same shi da cutar.

https://p.dw.com/p/3jpJP
USA | Wahlkampfkundgebung | Friedlicher Protest | Washington
Hoto: Tom Brenner/Reuters

Shugaban ya fara gangamin na makwanni uku kafin zabe, da wani taro a filin jirgin saman jihar Florida.

Wannan taro dai shi ne gangami na farko da Trump ke halarta tun bayan da ya fito daga asibiti bayan ya kwashe kwanaki uku yana jinya cutar ta sarkewar numfashi. A jiya Lahadi shugaban ya bayyana cewar ya warke sarai daga cutar ta corona, sai dai bai bayyana gwajin da ya nuna cewa bayya dauke da cutar ba.

Masu sukar lamairin shugaban na ci gaba da nuna yatsa a kan gazawarsa ta nunawa magoya bayansa muhimmancin saka takunkumi da ma ajiye tazara a tsakaninsu.