1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaba Putin zai gana da shugabannin Afirka

July 26, 2023

A ci gaba da neman hanyoyin yaukaka alaka tsakaninta da kasashen Afirka, gwamnatin Rasha ta shirya taro da zai dubi hanyoyin inganta abubuwan da take muradi.

https://p.dw.com/p/4UR5L
Hoto: Gavriil Grigorov/TASS Host Photo Agency/dpa/picture alliance

Shugaba Vladimir Putin na kasar Rasha, na shirin karfafa alakarsa da kasashen Afirka musamman a lokacin taron koli da zai yi da shugabannin nahiyar a birnin St. Petersburg.

Taron shugabannin za su yi na yini biyu, zai dubi batutuwa ne na tattalin arziki da kuma ayyukan jinkai.

Haka nan Shugaba Putin ya shirya ganawa da shugabannin na Afirka a game da neman sasanta rikicin da ke tsakaninsa da Ukraine.

A gobe Alhamis ne dai za a fara taron kuma wakilai daga kasashen Afirka 49 sun sanar da shirinsu na halarta.

A share guda kuwa ministan harkokin wajen Ukraine, Dmytro Kuleba zai kai ziyara kasar laberiya, ziyarar da ke ta uku ke nan da yake kaiwa nahiyar Afirka tun bayan fara yaki a kasar.