Shugaba Mursi na Masar na rangadi a Sudan
April 5, 2013Shugaban ƙasar Masar Mohammed Mursi ya na ran gadi na wuni biyu a maƙociyar ƙasarsa wato Sudan domin inganta dangantaka ta tattalin arziƙi, a wani abunda ake gani na da tarihi duk da cewa yana zuwa ne kusan shekara guda da zaɓen Morsi a matsayin shugaban ƙasa.
Wannan ce ziyararsa ta farko a Sudan wacce Ƙasar Masar ta mulka tare da haɗin gwuiwar Burtaniya har zuwa shekarar 1956
Ofishin shugaba Mursi, ya ce wannan ziyara na da mahimmanci sosai kasancewar ita ce ta farko irinta, da ma burinta na ƙara danƙon dangantakar da ke tsakanin ƙasahsen biyu musamman a fanin noma, cuɗanya da kasuwanci, da ma mafi mahimmanci yarjejeniyar da suka kira "four freedoms" a turance wacce ta tanadi baiwa, 'yan asalin ƙasashen biyu, 'yancin shiga da fita ƙasashen na su dan gudanar da cinikayya da sauran harkokin da suka danganci bunƙasa tattalin arziƙi.
To sai dai Amurka ta sanyawa Sudan takunkumin kasuwanci tun a shekarar 1997 bisa dalilan da Washington ta ce sun haɗa da take 'yancin bil adama
Mawallafiya: Pinado Abdu Waba
Edita: Mohammed Awal Balarabe