1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Tanzaniya ya rage albashin jami'an gwamnatinsa.

Ramatu Garba Baba
October 4, 2017

Shugaba John Magufuli na kasar Tanzaniya shi ne shugaban kasa a Afirka mai karbar albashi na dala dubu hudu a wata guda bayan ya zabtare rabin kudin da ya kamata ya karba a wata.

https://p.dw.com/p/2lCqk
Tansania John Pombe Magufuli Präsident
Hoto: DW/S. Michael

Shugaban John Magufuli ya sanar da rage albashin manyan mukaraban gwamnatinsa inda ya kuma bukaci wadanda suka ki amincewa da matakin da su gaggauta ajiye mukaminsu, Magufuli ya kuma yi watsi da bukatar wasu daga ciki na neman karin alawus bisa wasu dalilai na rashin abubuwan more rayuwa da ya ce al'ummar kasar ke fuskanta, ya kuma kare matakin rage albashin ganin yadda wasu bayanai ke nuni da cewa akwai wasu 'yan tsiraru da ke wawashe kudadden gwamnati.

Shugaban ya kuma baiyana cewa albashinsa a wata guda dala dubu hudu ne kacal bayan ya rage albashin da ya kamata ya karba, hakan na nufin shi ne shugaban Afirka mafi kankantan albashi a nahiyar. Tun bayan dare karagar mulki a shekarar 2015, Magufuli y ke yaki da masu yin almundahana da kudadden gwamnati a kasar ta Tanzaniya.