1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaArewacin Amurka

Shugaba Biden na Amurka da Donald Trump sun caccaki juna

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
March 10, 2024

Mr Trump ya ce ya tsallake duk wani tarko da Biden din ke 'dana masa don kawar da shi

https://p.dw.com/p/4dM5V
Hoto: ABACA/IMAGO;AP Photo/picture alliance

Shugaba Joe Biden na Amurka da tsohon shugaban kasar Donald Trump sun caccaki juna a yakin neman zaben da suka gudanar a jihar Georgia a ranar Asabar, domin tunkarar babban zaben kasar da za a gudanar a ranar 5 ga watan Nuwamba mai zuwa.

Karin bayani:Joe Biden da Donald Trump na yakin neman zabe a Georgia

Mr Biden ya zargi Donald Trump da kulla alaka da masu aikata miyagun laifuka, yana mai danganta ganawar da ya yi da firaministan Hungary Victor Orban a matsayin son kai da kuma kusanci da 'yan kama-karya.

Karin bayani:Biden ya caccaki Donald Trump

A nasa bangaren Mr Trump, ya ce ya tsallake duk wani tarko da Biden din ke 'dana masa don kawar da shi.