1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaba Biden ya kamu da Corona

July 22, 2022

Fadar White House da da ke kasar Amirka ta tabbatar da cewa bayan wani gwaji da aka yi wa shugaban kasar, an same shi da kwayar cutar sarkewar numfashi ta Coronavirus.

https://p.dw.com/p/4EV0W
USA | Coronavirus | Ankündigung COVID Strategie | Präsident Joe Biden
Hoto: Kevin Lamarque/REUTERS

Shugaban Amirka Joe Biden ya kamu da kwayar cutar Corona, kamar yadda fadar White House ta tabbatar.

Shugaba Biden wanda ke da shekaru 79 a duniya, ya harbu da Coronar ne bayan sakamkon gwajin da ya yi ya tabbatar da hakan.

Shugaban na Amirka ya ce akwai wasu kananan alamun cutar a tare da shi, sai dai kuma ba ya jin wata gagarumar rashin lafiya a yanzu.

Tuni kuma ya ce ya fara shan maganin cutar mai suna paxlovid.

Likitan shugaban na Amirka, Dr. Kevin O'Connor, ya ce Mr. Biden na fama da kasala da mura gami da tari ne tun da yammacin ranar Laraba.