1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirye-shiryen bukin samun 'yancin kai a Kudancin Sudan

July 8, 2011

Amurka ta yi alƙawarin cire takunkumin da ta sanya wa Sudan daga yankin kudancin da zarar ta kammala bukin kafa gwamnatin ta.

https://p.dw.com/p/11rIm
Hoto: DW

A yayin da yankin kudancin Sudan ke shirin gudanar da bukin kafa gwamnatin cin gashin kanta a ranar Asabar, hukumomi a Amurka sun ce za su cire takunkumin da suka sanya wa ƙasar a yankin kudancin bayan kammala bukin 'yancin kai. Jakadar Amurka a Majalisar Ɗinkin Duniya Susan Rice wadda zata jagoranci tawagar da za ta wakilci Amurka a bukin na ranar Asabar a birnin Juba, ta faɗa wa wani taron manema labarai cewa fadar gwamnati a Washington na iya ƙoƙarin ta wajen ganin sabuwar ƙasar ta sami bunƙasar tattalin arziƙin ta nan ba da daɗewa ba. Ta kuma nemi gwamnati a Khartoum da ta canza shawarar ta na fitar da dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya daga ƙasar bayan bukin, tana mai cewa akwai batutuwa da dama dake tattare da hatsari musamman ma tsakanin iyakokin yankunan biyu. Ita dai Amurkar ta yi alƙawarin gudanar da wani taron ƙoli na ƙasa da ƙasa a Juba a watan Satumba mai zuwa inda za ta ƙaddamar da wasu shirye-shiryen da za su samar da ci-gaba a ɓangaren gwamnati da na 'yan kasuwa. Kuma tun a bara ta yi wa sabuwar ƙasar alƙawarin tallafi na kuɗi dala milliyan 300 kuma ana sa ran za ta ƙara bada wani tallafin a lokacin taron na watan Satumba.

Mawallafiya: Pinado Abdu
Edita: Mohammad Nasiru Awal