A cikin shirin za a ji cewa, kasashe biyar na Afirka sun shirya tura wata rundunar yaki da ta'addanci ta hadin gwiwa a yankin Sahel, rundunar za ta yi aiki tare da ta Majalisar Dinkin Duniya, sannan za a ji halin da ake ciki a Nijar bayan rufe gidan rediyon Alternative mai zaman kansa.